Shugaban ‘yan sandan yankin nan na Indonesia da aka samu turmutsutsu a filin wasan kwallon kafa da mutane da dama suka mutu a ranar Asabar ya nemi afuwa.
Nico Afinta ya ce bai ji dadi da aukuwar lamarin ba, sannan ya ce yana fatan jama’a za su yi musu afuwa.
Akalla mutane 125 ne suka mutu a lokacin da mutane suka nufi kofar fita daga filin wasan, bayan ‘yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye.
Hukumar kwallon kafa ta kasar ta hana jami’an kungiyoyin kwallon kafar da suka yi wasa a ranar shiga wasanni har abada, tana mai cewa sun gaza gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.