Hukumomin lafiya a kasar, Tanzania, sun haramta sayar da wani fitaccen maganin karfin maza na gargajiya mai suna Hemsha, da ‘yan magori ke cin kasuwarshi a kasar.
Shugaban kwamitin kungiyar masu maganin gargajiya da amfani da su Farfesa Hamisi Malebo, ya ce an dauki matakin haramta amfani da maganin, ya biyo bayan binciken da aka gudanar.
Ya ce gwajin da jami’an lafiya suka yi kan maganin gargajiyar, sakamako ya nuna akwai akwai burbushin maganin karfin maza da aka bi sani da Viagra.
Ya kara da cewa bai dace maza su dinga amfani da maganin Hemsha ba, saboda zai hukumar da ke sa ido kan ingancin magunguna ta kasar ba ta aminta da shi ba.
Maganin karfin mazan an yi shi ne da wasu ganyayyaki da itatuwa da bawon bishiyar Mkongo da aka fi samu a yammacin Afirka.
Haka kuma ‘yan sari, na sauya masa suna da tambarin da suka ga dama a jiki.
Tuni aka bukaci masu sarrafa maganin na Hemasha su dakatar da yi nan take, da dakatar da saidawa ga abokan hulda.
Farfesa Malepo, ya ce karfafa gwiwar saidawa mutane maganin gargajiya ba tare da hukumar lafiya ta aminta da ingancinsa ba, babban laifi ne.
A shekarar 20202 ne Tanzania, ta bai wa ‘yan kasar kwarin gwiwar amfani da wasu magungunan gargajiya guda biyar da nufin karawa maza kuzari lokacin jima’i. A cewar BBC.