Wasu jihohi a Indiya sun fara haramta sayar da alewar yara ta “Sweet Camfo.”
A satin daya gabata ne Jihar Tamil Nadu dake Kudancin ƙasar ta saka dokar hana sayar da alawar bayan tabbatar da samun sinadarin da ke haddasa cutar cancer na Rhodamine-B a ciki yayin gwaji.
Farkon watan nan ne wata ƙungiya a yankin Puducherry ta haramta alewar yayin da da wasu jihohin suka fara gwajin samfuranta.
Alewar ta ‘Sweet Camfo’ da ake kira da buddi-ka-baal a Indiyance wanda ke nufin gashin tsohuwa sananniya ce tsakanin yara a duk faɗin duniya.
Ana samunta a wajen wasan yara da sauran wuraren bukukuwa da yara kan halarta.
Alewar na da farin jini tsakanin yara saboda yadda take kamar auduga sannan take narkewa da sauri a baki.
Amma wasu hukumomi a Indiya sun ce haɗarinta ya fi yanda ake tsammani.
A satin daya gabata jami’an jamai’a Hukumar Kula da Tsaftar Abin ta kasar suka kai wa masu sayar da alewar samame a bakin teku da ke birnin.
Bincike ya nuna cewa sinadarin na Rhodamine-B da ake samu a alewar na ƙara haɗarin kamuwa da cutar cancer sannan ƙasar Birtaniya da California sun haramta amfani da shi wajen busar da abinci