fidelitybank

An haramta hada-hadat kudaden Intanet na Binance

Date:

Hukumar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya, ta haramta ayyukan kamfanin hada-hadar kuɗaɗen intanet na Binace a ƙasar.

Matakin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar ta hukumar ta wallafa a shafinta intanet.

Hukumar hada-hadar hannayen jari ta ƙasar ta ce kamfanin na Binance bai yi rajista da ita ba, a don haka ne ta ce ta haramta ayyukan kamfanin a fadin ƙasar.

Sanarwar ta kuma gargaɗi ‘yan ƙasar da ke mu’alama da kamfanin da su dakata, in ba haka ba kuwa duk abinda ya same su to su kuka da kansu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa ”An nusar da hukumar kula da hada-hadar hannayen jari ta Najeriya game da shafin intanet da kamfanin Binace ke gudanarwa, inda yake neman ‘yan Najeriya da su zuba jari kan harkar hada-hadar kuɗin intanet na cyrpto a shafin nasa da wasu manhajojin wayar hannu.

Kan haka ne hukumar ce bayyana wa ‘yan ƙasar cewa ”kamfanin ‘Binance Nigeria Limited’ ba shi da rajista da hukuma, kuma baya aiki da dokokin hukumar kula da hannayen jari ta ƙasar, don haka duk abin da ya samu mutumin da ke mu’amala da kamfanin to ya kuka da kansa”.

Hukumar ta kuma shawarci ‘yan ƙasar da su guji zuba jari a harkar hada-hadar kuɗaɗen intanet ta crypto a kamfanonin da ba su da rajista da hukumar.

Hukumar kula da hada-hadar hannayen jari ta Najeriyar ta buƙaci kamfanin ‘Binance Nigeria Limited’ da ya gaggauta dakatar da ayyukansa a faɗin ƙasar.

Hukumar ta kuma ce za ta bayyana matakan ladabtarwa da za ta ɗauka kan kamfanin da wasu takwarorinsa marasa rajista a ƙasar.

Ta ƙara da cewa za ta yi aiki tare da hukumomin da lamarin ya shafa a ƙasar domin ɗaukar mataki game da batun.

A makon da ya gabata ne dai Hukumar kula da kasuwar hannayen jari ta Amurka ta shigar da ƙarar kamfanin na Binance a gaban kotu.

A ranar Alhamis ne kuma kamfanin ya ce ya dakatar da hada-hada da kuɗin dala na Amurka bayan matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka a kansa.

Wannna mataki dai ka iya kawo cikas ga kasuwar hada-hadar kuɗi ta intanet wato crypto a Najeriya, musamman ganin cewa a baya-bayan hukumar kula da kasuwar hannayen jari ta ƙasar ta haramta ayyukan kamfanin Paxful.

www.nigerianews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp