Rundunar ƴan sanda a Zamfara ta haramta taruka da gangamin siyasa gabanin hukuncin kotun ƙoli kan zaɓen gwamnan jihar.
Kwmaishinan ƴan sanda na jihar Zamfara, Muhammad Dalijan ne ya sanar da haramcin yayin da ake dakon hukuncin da kotun ƙolin za ta yanke kan ƙarar da gwamna Dauda Lawal ya shigar gabanta inda yake neman a soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ya buƙaci a sake zaɓe a jihar.
Kwamishinan ƴan sandan ya kuma ja kunnen magoya bayan jam’iyyar APC da na PDP da su guji furta kalaman da ka iya yamutsa hazo.
Ya ce jami’an tsaro za su sa ido tare da hukunta duk wanda aka samu da tada hayaniya a jihar.
A cewarsa, an baza ƴan sanda a lungu da saƙo na jihar domin tabbatar da doka da oda inda kuma ya nemi jama’ar jihar da su ci gaba da tafiyar da harkokinsu.