Hukumomi a jihar Filato sun sanar da sanya dokar hana zirga-zirga a yankin Bwai na ƙaramar hukumar Mangu.
Wata sanarwa da ta samu sa hannun shugaban ƙaramar hukumar Mangu, Minista Daput, ta ce an amince da sanya dokar ne domin dawo da zaman lafiya, bayan wani hari da aka kai wanda ya yi sanadin rayukan kimanin mutum 20.
Bayanai sun nuna cewa wasu mahara ne suka far wa ƙauyukan da asubahin ranar Talata inda suka cinna wa gidaje wuta.
Haka nan maharan sun riƙa far wa al’umma da ke ƙoƙarin tserewa, wanda hakan ya haifar da mutuwar mutane da dama da kuma raunata wasu.
Ya zuwa yanzu an gano gawarwaki kimanin 20 a ƙauyukan Fungzai da Kubat.
Bayanan sun ƙara da cewa ana ci gaba da bincike domin gano ko akwai sauran waɗanda suka mutu ko suka raunata a sanadiyyar harin.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda a jihar ta Filato, DSP Alfred Alabo ya ce sun tura da ƙarin jami’ansu domin tabbatar da zaman lafiya da gudanar da bincike.