Ana jin ƙarar harbe-harbe a Freetwon babban birnin Saliyo da sanyin safiyar yau Lahadi.
Mazauna birnin sun ce sun ji ƙarar harbe-harben ne daga aƙalla barikokin soji biyu.
Tuni hukumomi suka sanya dokar hana fita a faɗin ƙasar baki ɗaya wadda ta fara aiki nan take.
Cikin wata sanarwar da ma’aikatar yaɗa labaran ƙasar ta fitar, ta ce wasu mutanen ne da ba a son ko su wane ne ba, suka yi yunƙurin shiga barikokin sojin ƙasar na Wilberforce da ke birnin Freetown
Sanarwar ta ce jami’an tsaro sun samu nasarar fatatakar ‘yan bindigar.
A baya-bayan nan ƙasashen yankin Yammacin Afirka na fuskantar barazanar juyin mulki, inda a cikin shekara uku aka samu juyin mulkin soji a wasu ƙasashen yankin, ciki har da Guinea mai makwabtaka da Saliyo.