Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga 12 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, da suka hada da sarkinsu, ‘Madaki Mansur’ da ke addabar mazauna karamar hukumar Alkaleri, da sauran jihohin da ke makwabtaka da Taraba, Filato da Gombe.
Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Wakili ya fitar ta ce, “a kokarin da muka yi na dakile matsalar ‘yan bindiga a jihar Bauchi, musamman a karamar hukumar Alkaleri, rundunar ta kasance mafi kyawu a kwanan nan.”
A cewarsa, a ranar 19 ga watan Disamba, 2022, da misalin karfe 0230 na safe, rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro ta kama wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne masu garkuwa da mutane a maboya daban-daban guda hudu: Mansur, Digare, Gwana da Dajin Malam a dajin Alkaleri.
Ya kara da cewa, biyo bayan musayar wuta da jami’an suka yi, an kashe 12 daga cikin masu garkuwa da mutane, yayin da wasu kuma aka fatattake su, aka tarwatsa su, sannan suka ruguza cikin dazukan da ke kusa da inda aka samu raunukan harbin bindiga.
An gano makamai da babura masu aiki a yayin aikin.