Ƴan sanda a Afghanistan sun tabbatar da mutuwar mutane biyar a wani hari da aka kai wa ma’akatan wani kamfanin mai da ke cikin motar Bus kan hanyarsu ta zuwa wurin aiki.
Lamarin dai ya faru ne a yankin arewacin kasar ta Afghanistan.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ma’aikatan huɗu sun ji mummmunan rauni. In ji BBC.
Mai magana da yawun ƴan sandan yankin Balkh, ya ce hatta motar da harin ya rutsa da ita ta kamfanin mai na Hairatun ne.
A baya-bayan nan dai ana yawan kai hare-hare a biranen Afghanistan, yawanci kuma kungiyar masu kaifin kishin islama ta IS ke daukar alhakin kai wa.