An haifi jariri a cikin jirgin sama yayin da yake tafiya a sama a hanyarsa ta zuwa birnin Alkahira na Masar daga birnin Jiddah na Saudiyya ranar Lahadi.
Iyayen yaron daga Masar na farin cikin samun sabon jariri, wanda ya zama karin fasinja a jirgin yayin da ya sauka a birnin Cairo.
Mai jegon ƴar shekaru 26 ta fara naƙuda ne a lokacin da jirgin yake keta hazo a samaniya.
Ma’aikatan jirgin sun yi zafin nama wajen taimaka mata tare da samun agajin wani likita da ke cikin jirgin.
Sun taimaka wa mai naƙudar wajen haihuwa ba tare da matsala ba. Mahaifiya da jaririn sun sauka a cikin ƙoshin lafiya.
Biyo bayan saukar jirgin a babban filin jirgin saman Cairo, motar asibiti ta tarbi jirgin inda ta gwada lafiyar uwa da jaririn, sannan ta dauke su zuwa asibiti domin a cigaba da duba lafiyarsu. In ji BBC.