Rundunar ‘yan sanda a Legas ta gurfanar da wasu mutane biyu, Ifeanyi Chukwu da Amadi Orji a gaban wata kotun Majistare ta Ojo da ke Legas, bisa zargin su da satar tukunyar iskar gas.
Chukwu, mai shekaru 42 da Orji, mai shekaru 50, suna gurfana a gaban kotun Majistare, Mista LK J Layeni, bisa tuhume-tuhume biyu da suka shafi hada baki da sata.
Sai dai sun musanta zargin da ake musu.
Tun da farko dai mai gabatar da kara, Dokta Simon Uche ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a watan Disambar 2022, a sashen Fancy and Furniture na kasuwar kasa da kasa ta Alaba da ke Ojo, Legas.
Ya kara da cewa wadanda ake tuhumar sun hada baki ne wajen satar iskar gas mallakin wani Victor Nzekwe, inda ya kara da cewa kudin silinda din ya kai Naira miliyan 20.
A cewarsa, daga karshe ‘yan sanda sun cafke wadanda ake tuhuma tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Laifin a cewarsa ya sabawa tanadin sashe na 287 da na 411 na dokar laifuka ta jihar Legas 2015.
Don haka Alkalin kotun ya bayar da belin wadanda ake tuhumar a kan kudi Naira miliyan daya kowanne tare da masu tsaya masa guda biyu kowannensu a daidai wannan adadi sannan ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 7 ga watan Fabrairun 2024 domin ambato.