fidelitybank

An gurfanar da wata mata a kotu saboda ta saka danta karami a matsayin soja

Date:

Wata kotu a kasar Sweden ta tuhumi wata mata ‘yar kasar  da aikata laifukan yaki saboda ta taimaka wajen sanya danta mai shekaru 12 a matsayin sojan a kasar Syria, inda a ka kashe shi a yakin basasar da su ke tafkawa.

Kamfanin dilancin labarai na Reuters ya rawaito cewa, matar mai shekaru 49, ‘yar kasar Sweden da ta dawo daga kasar Syria a shekarar 2020, ita ce mutum ta farko da a ka sani da a ka tuhume ta a Sweden da laifin taimakawa daukar karamin danta a matsayin soja.

Yaron, wanda a ka haifa a shekara ta 2001, ya fara gwagwarmaya ne tun a shekara ta 2013, domin shiga kungiyoyin da su ka hada da na IS. Ya kuma mutu a cikin shekarar 2017, sai dai hukumomi ba su fitar da wani karin bayani game da mahaifiyar ko ɗanta ba.

A zaman kotu na ranar Talatar nan, matar ta musanta zargin, ta hannun lauyanta, Mikael Westerlund.

Sai dai kotun ta ce har Idan a ka same ta da laifi za ta fuskanci hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari, inji mai gabatar da kara Reena Devgun.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, daukar yara ‘yan kasa da shekaru 15 aiki da kuma amfani da su a matsayin sojoji haramun ne a karkashin dokar jin kai ta kasa da kasa, kuma kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta amince da shi a matsayin laifin yaki.

A karkashin dokar Sweden, kotuna na iya yi wa mutane shari’a da laifukan da su ka saba wa dokokin kasa da kasa da a ka aikata a kasashen waje. Za kuma a ci gaba da shari’ar ne a ranar Litinin 10 ga watan Janairu.

nnnnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp