Wata Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano ta tsare wani Nura Musbahu tare budurwarsa sa Fatima Lawal bisa laifin satar kayan lefe na ‘yar uwarsa Aisha.
A zaman kotun da ke Rijiyar Lemo a karamar hukumar Fagge, inda aka tuhume su da laifin sata da kuma karbar kayan da aka sace.
A lokacin da jami’in kotun, Usman Idris Shu’aibu Dala ya karanta musu tuhume-tuhumen, Musbahu ya amsa laifinsa.
Sai dai budurwar tasa ta yarda cewa abubuwa biyu ne kawai aka ba ta, wadanda ta gabatar da su a gaban kotu.
Daga nan sai Khadi Danbaba ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare su a gidan gyaran hali har zuwa ranar 5 ga watan Yuni, 2024, sannan ya umurci iyayensu su bayyana a gaban kotu.