fidelitybank

An gurfanar da mai karbar kudi a kotu da wasu alkalai akan zargin cinye kudin marayu

Date:

An gurfanar da wata mai karbar kudi a kotun shari’ar Musulunci ta Jihar Kano, Hussaina Imam da wasu mutum 14 da suka hada da alkalai da masu rijista a gaban wata kotun majistare da ke jihar bisa zargin karkatar da zunzurutun kudi har Naira miliyan 500 da aka ware wa marayu.

A lokacin gudanar da shari’ar ranar Laraba a gaban Alkalin Kotun Mai shari’a Mustapha Sa’ad Datti, an zargi wadanda ake tuhumar da aikata laifin da ya shafi hada baki da cin amana da ma’aikatan gwamnati da kuma sata.

Mai shari’an ya ce laifin ya saɓawa sashe na 97 da 79 da 315 da 289 na kundin Penal Code.

Rahoton farko da aka fitar, ya nuna cewa wadanda ake zargin, Bashir Ali Kurawa da Saadatu Umar da Tijjani Abdullahi da Maryam Jibrin Garba da Shamsu Sani da kuma Hussaina Imam, sun aikata laifi a shekarar 2020/2021, inda Imam ta yi amfani da mukaminta na mai karɓar kudi a kotun daukaka kara ta shari’ar musulunci ta jihar Kano wajen hada baki da wasu.

Ana zargin ta da laifin buga jabun wasikun kotun Shari’a tare da sace kudi har naira miliyan ɗari hudu da tamanin da takwas da ‘yan kai mallakin kotun daukaka karar shari’ar Musulunci ta jihar Kano.

Sai dai duk waɗanda ake zargi sun musanta aikata laifin da ake tuhumar su da shi, inda lauyan da ke kare su ya bukaci kotu ta bayar da belin su.

naija hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp