Da alama yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ayyana tsakanin ɓangarorin mayaƙa biyu da ke gumurzu da juna a Sudan, domin bikin Idin babbar sallah, ta ruguje.
Wata mai aikin agaji, Duaa Tariq ta shaida wa BBC cewa an rinƙa jin rugugin manyan bidigogi a wasu sassa na Khartoum, babban birnin ƙasar tun da sanyin safiya.
A ranar Talata, shugaban gwamnatin mulkin sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan ya yi kira ga matasa da shiga yaƙin da ake yi da mayaƙan RSF.
Sai dai Ms Tariq ta shaida wa BBC cewar dakarun RSF ɗin ne suka fi yawa a Khartoum, inda suka mamaye gidaje da kasuwanni da kuma titunan birnin.
Wasu yarjeniyoyin da aka cimma a baya duk sun samu matsala a faɗan wandsa aka kwashe mako goma ana gwabzawa.