fidelitybank

An gudanar da addu’o’in samun sauƙin rayuwa a Kano

Date:

Duk da kiraye-kirayen da aka rinƙa yi na neman a ɗage addu’o’i na musamman da aka tsara za a fara yi daga yau Asabar a Najeriya, bayanai sun nuna cewa an gudanar da addu’ar a masallacin, gidan Isiyaku Rabi’u da ke Goron Dutse, a yankin, ƙaramar hukumar Dala, da ke Kano.

Jaridar daily Trust ta ruwaito cewa, wani mai amfani da shafukan sada zumunta da muhawara ya sanya a shafinsa na Facebook cewa: ”Ana karatun Qur’ani daga nan masallacin Khalifa Isyaku Rabiu, Goron Dutse, Kano, domin addu’a kan halin da kasarmu ke ciki, Allah Ya sawƙaƙa mana, Amin.”

Daman jaridar ta ruwaito cewa, ɗaya daga cikin mutanen da suka shirya addu’ar ƙasa da za a fara yau Asabar 10 ga watan Agusta, 2024, a masallacin na Isiyaku Rabi’u, da kuma sauran jihohin ƙasar, Mubarak Ibrahim Lawan, ya sanar da cewa an fasa saboda dalilai na tsaro, ganin yadda zanga-zangar lumana da aka fara a ranar 1 ga watan nan na Agusta ta tsawon kwana goma ta rikiɗe a wasu jihohin ta zama tarzoma, inda aka rinka sace-sace da ɓarnata dukiya ta gwamnati ta ‘yan kasuwa da sauransu, har ma da kisa da raunata jama’a, wanna ya sa wasu suka yi, tunanin karkata ga addu’a domin samun sauƙi a kan matsalolin da ke addabar ƙasar.

A wani saƙo na bidiyo da ya fitar, a Kano, Mubarak, ya ce, kwamishinan ƴansanda na jihar, da kuma darektan hukumar tsaro ta DSS shi ma na jihar sun ankarar da su cewa wasu ɓata-gari a ƙasar sun shirya tura wasu miyagu wajen taron addu’ar, domin cimma manufarsu.

Ya ce, an yi zargin cewa za su jagoranci wasu matasa da za su riƙa kwashe kayan jama’a da na hukuma, da sace-sace, kamar yadda aka yi a baya a lokacin da aka fara zanga-zanga, a saboda haka ya ce sun fasa taron addu’o’in.

sun newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp