fidelitybank

An gayyaci Malamin da ya furta ba ya buƙatar ɗaukin Annabi S.A.W

Date:

Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi, ta shirya muƙabala tsakanin malamai da kuma Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi, kan kalaman da ya yi game da Annabi Muhammadu (SAW).

Wata wasiƙa da hukumar ta aike wa malamin, ɗan asalin jihar Bauchi, ta ce za a gudanar da tattaunawar ilimin ne gobe Asabar, 8 ga watan Afrilu a birnin Bauchi.

A farkon makon nan ne kalaman malamin suka fara tayar da hazo musamman a shafukan zumunta, bayan ya yi iƙirarin cewa “ba ya buƙatar taimakon Annabi”.

“Ana gayyatar ka zuwa tattaunawa ta ilimi [munaƙasha] game da kalamanka cewa ‘kai! …Manzon Allah ma ba ma son taimakonsa, ƙarewarta kenan’,” kamar yadda hukumar ta bayyana cikin wasiƙar.

Bauchi Cleric

An ga malamin ya bayyana cikin wani bidiyo a ranar Alhamis yana cewa ya ji daga wata majiya cewa zai yi muhawara da wakilan wasu ƙungiyoyin addini a jihar, waɗanda suka haɗa da Izala da ɗariƙa.

An yi irin wannan muhawara a Kano cikin watan Yulin 2021 lokacin da aka zargi Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammadu.

Bayan muhawarar ne kuma, hukumomi suka gurfanar da malamin a gaban kotu, wadda ta yanke masa hukuncin kisa. In ji BBC.

the sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...
X whatsapp