Babban Lauyan Najeriya, SAN, Jibrin Samuel Okutepa, ya gargadi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a kan tura sojojin Najeriya domin warware rikicin jamhuriyar Nijar.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne Tinubu ya aike da wasika zuwa ga majalisar dattawan Najeriya, inda ya nemi amincewar daukar matakin soji da sauran takunkumi kan jami’an sojin da suka kwace mulki a Nijar.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar a zauren Majalisar.
Sai dai Okutepa, a wasu jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter a safiyar ranar Asabar, ya yi fatan majalisar dokokin kasar ba za ta amince da bukatar Tinubu na tura sojojin Najeriya zuwa Nijar domin yakar ‘yakin da ba shi da ma’ana’ na maido da mulkin dimokradiyya a kasar.
Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “Ina fata kawai majalisar dokokin kasar ba za ta amince da bukatar tura sojojinmu zuwa jamhuriyar Nijar domin yaki da rashin imani na maido da mulkin dimokradiyya a kasar ba.
“Yan Najeriya na bukatar hukumomin tsaron mu da suka hada da sojoji domin dawo da zaman lafiya da tsaro a Najeriya.”
A halin da ake ciki dai gwamnatin mulkin sojan Nijar ta katse huldar diflomasiyya da Najeriya bayan da wakilin ECOWAS da ta aika zuwa kasar domin samar da zaman lafiya ya kasa cimma wani sakamako.
A watan da ya gabata ne dai gwamnatin mulkin soji ta hambarar da zababben shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum.