Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohin Borno, Jigawa da Yobe, kamar yadda Hukumar Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta sanar a wani hasashen yanayi da ta fitar a shafinta na X.
Hukumar ta ce tsawa da ruwan sama matsakaici na iya sauka a wasu sassan arewacin Najeriya wadda zai iya haddasa ambaliyar ruwan.
NiMet ta bayyana cewa da safiyar yau Talata, ana sa ran ruwan sama a jihohin Borno, Yobe, Jigawa, Gombe, Bauchi, Adamawa, Kaduna da Taraba.
Hakanan, da yamma zuwa dare, ana sa ran yawancin jihohin Arewa za su ci gaba da samun ruwan sama tare da iska da tsawa.
A tsakiyar Najeriya kuwa, hasashen ya nuna cewa za a samu yanayin giragizai da safe, sannan da yamma za a samu ruwan sama matsakaici a wasu sassan Nasarawa, Benue, Kogi, Kwara, Neja, Filato da kuma babban birnin tarayya Abuja.
NiMet ta kuma bayyana cewa a Kudancin Najeriya, da safe ana sa ran yanayi mai giragizai tare da yiwuwar ruwan sama a wurare kaÉ—an, yayin da a Yammaci ake hasashen ruwan sama a lokuta daban-daban.
Hukumar ta yi gargaɗi ga al’ummar da ke zaune a wuraren da ke da haɗarin fuskantar ambaliya da su ɗauki matakan kariya. Ta kuma shawarci hukumomin agaji da sauran masu ruwa da tsaki da su kasance cikin shiri domin bada taimako idan buƙata ta taso.