Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan sama a wasu sassan kasar nan yanzu haka, hukumar kula da madatsun ruwa da kuguna ta ƙasar, NiHSA ta yi gargaɗin samun mummunar ambaliya a ƙananan hukumomin 198 cikin jihohi 31 tsakanin 7 zuwa 21 ga watan Agustan da muke ciki.
Cikin wata sanar wa hukumar ta fitar, ta ce fiye da garuruwa 832 ne ke cikin hatsarin fuskantar ambaliyar.
Hukumar ta kuma yi gargaɗin lalacewar tituna fiye da 100, yayin da ake fargabar ambaliyar za ta tilasta wa mutane barin gidajensu.
Gargaɗin na zuwa ne bayan da farkon makon nan hukumar ta yi gargaɗin samun ambaliyar a jihohin ƙasar 19.
Tuni dai wasu jihohin suka fara fuskantar ambaliyar.
Gargaɗin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Legas ke jajanta wa mazauna unguwar Ikorodu sakamakon mamakon ruwan sama da ake samu a yankin tun daga ranar Litinin da ta gabata.