Wani babban jami’in lafiya a Amurka ya fitar da gargadi kan hadarin shafukan sada zumunta ga yara da matasa.
Dr Vivbek Murthy, wanda shi ne shugaban ma’aikatar lafiya ta Amurka ya ce, kafofin sada zumunta da muhawara da kananan yara da matasa ke amfani da su na haifar da manyan kalubale ga lafiyar jiki da rayuwarsu.
Sannan suna haddasa matsalar rashin cin abinci da jefa masu amfani da su cikin damuwar rashin yarda da kai.
Rahoton ya ce matakan da ake dauka domin rage damar da yara ke da ita ko matasa a shafukan sada zumunta ba sa aiki.
Sannan kuma akwai sauran jan aiki a binciken gano cikakken tasirin da wadannan shafuka ke yi a rayuwar matasa.
Sai dai kuma duk da wannan gargaɗi masanin ya ce akwai wasu alfanu da waɗannan shafuka kan yi ga wasu rukuni na mutane a rayuwa. In ji BBC.