Masana ilimin albarkatun kasa a Israila sun gano wani masallaci, da ake tunanin na daya daga cikin masallatan da suka fi tsufa a duniya.
Karamin masallaci ne da aka gina da duwatsun da aka yi a tun karni na bakwai.
An gano masallacin ne yayin da ake aikin gina wani rukunin gidaje a birnin Rahat da ke Kudancin Isra’ila.
Kazalika alkiblar masallacin ta karkata ne zuwa birni mai tsalki na Makka.
Masallacin kuma na da nisan kilomita biyu ne daga wani masallacin irinsa, da ake tunanin an gina sune lokaci daya, wanda aka gano a 2019. A cewar BBC.