Jami’an tsaro na Civil Defence sun gano wani haramtaccen wurin tace danyen man fetur a wani daji mai kaurin suna a yankin Nembe da Akwa dake karamar hukumar Etche a jihar Ribas.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSC Babawale Afolabi ya fitar
A cewar sanarwar, bisa sahihin bayanan sirri, rundunar ta gudanar da wani gagarumin rangadin aiki na sama da sa’o’i 7, wanda ta bankado yadda ake gudanar da tace danyen man fetur din tare da lalata rijiyoyin,
Ya tabbatar da cewa rundunar, tun bayan kaddamar da aikin har zuwa yau, ta samu gagarumar nasara wajen yaki da satar danyen mai a fadin kasar nan, kamar yadda ya yaba da amincewar jama’a ga hukumar NSCDC ta hanyar sahihan bayanai.