Gwamnatin jihar Abia ta ce, ta gano gawawwakin wasu mutane sama da 50, ciki har da wadansu da ba su da kawuna guda 20, da kuma kwarangwal da dama a kusa da kasuwar shanu ta Lokpanta a garin Umunneochi.
Gwamnan jihar, Alex Otti ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai ta wata-wata a gidan gwamnati, yau Litinin, inda ya jaddada ƙudurinsa na magance matsalolin rashin tsaro a jihar.
Ya alaƙanta kai hare-hare a kasuwar, da matsaloli kamar karuwanci da fataucin miyagun kwayoyi da sauran miyagun ayyuka a yankin.
A matsayin martani, gwamnan ya bayyana cewa kasuwar Lokpanta za ta fara aiki a kullum daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.