Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya NRC a jiya ta ce, an gano 14 daga cikin fasinjoji 21 da aka sace a cikin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna.
Manajan Daraktanta, Mista Fidet Okhiria, ya yi karin haske kan harin da ‘yan ta’adda suka kai a yankin Kateri-Rijana da ke Jihar Kaduna a ranar 28 ga Maris.
Ya ce, fasinjoji 362 da aka tabbatar sun kasance a cikin jirgin da aka kai wa jirgin AK9 hari.
Ba a dai bayyana ko iyalan da aka sace mai mutane shida da kuma Manajan Daraktan Bankin Noma (BoA), Alwan Ali Hassan na daga cikin wadanda aka samu.