Masu bincike sun bayyana sakamako na farko-farko game da hatsarin jirgin saman Air India wanda ya yi ajalin mutum 260 cikin watan da ya gabata.
Bayanai da aka samu sun nuna cewa hanyoyin da ke kai mai ga injunan jirgin sun kasance a kashe jim kaÉ—an bayan tashinsa.
Yan dakiku bayan tashin jirgin saman kirar Boeing 787, maballan kunnawa da kashe mai sun kasance a kashe, lamarin da ya hana injinan jirgin samun mai, wanda ya kai ga daukewar lantarki a daukaci jirgin.
Kashe abin da ke kai mai zuwa ga injin jirgi abu ne da ke faruwa bayan saukar jirgin sama, sai dai ganin abin da ya faru, ya bar masu bincike cikin tababa.
A muryar da na’urar jirgin ta nada, an ji daya daga cikin matuka jirgin na tambayar dan’uwansa me ya sa ya kashe man, yayin da shi kuma ya mayar da martani da cewa ” ban kashe ba”.
Daga baya an kunna man, lamarin da ya sanya injinan jirgin suka fara aiki, sai dai a daidai lokacin da jirgin ya fadi kasa daya daga cikin injunan bai kammala dauka ba.
Lamarin dai baki daya ya faru ne a cikin ‘yan dakiku.
Yanzu haka dai masu bincike na ci gaba da nazarin karikitan jirgin da kuma na’urar nadan bayanai domin tantance duk abubuwan da suka faru gabanin hatsarin.
Kwararru a sufurin jiragen sama na kasar Indiya da kuma wasu daga kamfanin Boeing ne ke gudanar da binciken.
Yayin da wasu ke zargin cewa ko akwai yiwuwar wani ne ya yi abin da gangan, kamfanin jirgin saman ya ce matuka jirgin biyu sun tsalake duk wani gwaji da aka yi musu na cancanta kafin shiga jirgin, ciki har da gwajin shan kayan maye.
Sai dai yanzu masu bincike sun karkata ne domin gano ko maballan kunnawa da kashe man jirgin sun ci karo ne da matsala.