Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce ta yi nasarar gano ababen hawa 35 da aka sace a faɗin ƙasar cikin wata shidan farko na shekarar 2025.
Mai magana da yawun hukumar ta Federal Road Safety Corps (FRSC), Olusegun Ogungbemide, ya faɗa cikin wata sanarwa ranar Juma’a cewa sun yi nasarar ne sakamakon tsarinsu na rajistar ababen hawa ta intanet mai suna National Vehicle Identification Scheme (NVIS).
Ya ce an sace motocin ne ta hanyoyi daban-daban, ciki har da fashi, da garkuwa da mutane, da zamba.
“Domin tabbatar da nasarar yunƙurin, hukumar ta haɗa kai da sauran jami’an tsaro da kuma gwamnatocin jiha domin bin sawun ababen hawan,” in ji Mista Ogungbemide.