Masu aikin hakar ma’adinai a arewa maso gabashin Angola sun gano wani katon curin lu’u-lu’u da ba a taba ganin irinsa ba a kasar.
An yi imanin cewa katon curin lu’u-lu’un shi ne irinsa mafi girma da aka taba gani a doron kasa cikin shekara 300 a Angola.
Kamfanin hakar ma’adinai na kasar Australia wanda shi ne ya tono ma’adinin ya ce kamfanin sayar da ma’adinai na kasar Angola ne zai sayar da lu’u-lu’un a kasuwar ma’adinai ta duniya.
Gwamnatin Angola ta yaba da kokarin kamfanin wajen tono wannan ma’adini mai cike da tarihi. In ji BBC.