Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, ta ce jami’anta sun samu nasarar tarwatsa wani gungun ‘yan bindiga da ke kokarin kakaba dokar zaman gida a jihar.
Cikin wani sako da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce, a ranar Juma’a da safe ne jami’anta suka gano gawarwakin hudu daga cikin ‘yan bindigar a wani daji da ke garin Awkunanaw, inda suka gudu domin buya.
Sanarwar ta ce dama a ranar Alhamis, jami’a ‘yan sandan suka fatattaki wasu ‘yan bindiga da suka yi yunÆ™urin kwace wata mota daga hannun wani direba, inda maharan suka gudu tare da munanan raunukan harbin bindiga a jikinsu.
Daga nan ne kuma ‘yan sanda suka ce suka fara farautar maharan, inda suka gano makamai masu tarin yawa a lokacin binciken nasu
Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Ahmed Ammani ya tabbatar da cewa jami’an ‘yan sandan jihar da sauran jami’an tsaro ba za su yi kasa a gwiiwa ba har sai sun tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar, ta yadda mazauna jihar za su rika fita harkokin kasuwancinsu a kowacce rana.
Kungiyar masu tayar da kayar baya ta IPOB dai na tilasta wa mutane zaman gida a wasu ranaku, a wasu yankuna da ke kudu maso gabashin kasar.


