fidelitybank

An gano gawarwakin mutane 62 da jirgin sama ya hallaka su a Brazil

Date:

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Brazil ta gano dukkan gawarwakin mutanen da jirgin sama ya yi haɗari da su a kusa da birnin São Paulo, a ranar Juma’a.

Dukkan mutum sittin da biyu da ke cikin jirgin sun rasu, daga cikinsu akwai wata tawagar likitoci da ɗaliban jami’a da wasu iyalai uku da ke ƙoƙarin komawa gida daga wata ƙasa.

Bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda jirgin ya rikito daga sama zuwa ƙasa tare da kamawa da wuta.

Jirgin ya fado ne a wata unguwa da jama’a ke zaune, to amma ba wanda ya ji rauni a wajen da ya fado, sai dai jami’ai sun ce gida daya ya lalace.

Hukumomi sun ce gawarwakin – 34 na maza ne sai kuma 28 mata – kuma an kai su dakin ajiye gawarwaki na ‘yansanda a birnin na São Paulo, inda za a yi kokarin gano su tare da mika su ga iyalansu.

Tuni an riga an gane gawar matukin jirgin da ta mataimakinsa.

Iyalai da ‘yan uwan mutanen za su je domin taimakawa wajen gane gawarwakin.

Ana ci gaba da bincikin dalilin da ya haddasa hadarin.

legit.news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp