fidelitybank

An gano gawarwakin mutane 1,222 a Ukraine

Date:

Babbar mai shigar da ƙara a Ukraine ta ce gawar mutum 1,222 aka gano a wani yanki na birnin Kyiv tun bayan da dakarun Rasha suka fice daga yankin.

Iryna Veneditktova ta faɗa kafar talabijin ta Sky News cewa hukumomin Ukraine na bincike kan lamura 5,600 da ake zargin an aikata laifukan yaƙi, kuma tuni ta iya tantance laifukan yaƙi 500, ciki har da wanda suka ƙunshi manyan jami’an sojan Rasha da na gwamnatin ƙasar.

“Abin da muke gani a yankunan Ukraine laifukan yaƙi ne, da laifuka kan ɗan Adamtakar mutane, kuma muna yin duk abin da za mu iya don magance hakan,” a cewarta.

Ta ce, Ukraine na da hujjar da ke nuna Rasha ta kai harin makami mai linzami kan tashar jirgin ƙasa a Kramatorsk da ke gabashin ƙasar, wanda ya kashe mutum fiye da 50 da ke jiran ƙarasowar jirgin.

Rasha ta musanta hannu a harin na ranar Juma’a tana mai iƙirarin cewa, ba makaminta ba ne. Ta kuma musanta kai wa fararen hula hari.

bbc nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp