Ministan cikin gida na Ukraine Denys Monastiyaskai ya ce, masu bincike sun gano gawarwakin wasu fararen hula sittin da uku dukkaninsu da alamun gana musu akuba a jikinsu, a yankunan da ke karkashin da dakarun kasarsa suka kwato daga hannun Rasha.
Yankin na Kherson ya kasance karkashin ikon Rasha tsawon sama da wata takwas, mazauna birnin da suka yi nasarar tserewa daman sun bayar da rahotannin kisan jama’a da azabtarwa da kuma satar mutane da Rashawan masu mamaya suka yi.
Ministan ya ce hukumomin tsaro sun bankaɗo shaidu na laifukan yaƙi sama da 400 a lokacin mamayen na Rasha.
Amma ya ce yanzu ne ma aka fara neman mutanen da aka aikata laifukan a kansu.
Rasha dai ta musanta cewa dakarunta sun rika harar fararen hula ko kuma gana musu azaba, ko aikata ta’asa