An gano gawawwakin ‘yan ci-rani 61 da suka nutse a tekun Syria, a cewar ministan sufurin Lebanon.
Hukumomi sun ce daga cikinsu akwai ‘yan Lebanon da Syria d Falasdinu, kuma akwai mata da kananan yara, da ake zaton suna daga cikin mutum 120 zuwa 150 da ke cikin kwale-kwalen da ya kife ranar Alhamis.
Har yanzu ana kan aikin ceto da kuma kokarin gano abin da ya haddasa hadarin.
An kuma yi mutum 20 da aka samu a raye magani a asibitin birnin Tartus na Syria.
Ana zaton cewa kwale-kwalen zai tafi Turai ne kafin kifewarsa.
Yanzu haka akwai ‘yan gudun hijira miliyan daya da rabi a Lebanon, da suka guje wa yaki a Syria