An gano gawarwaki 213 da suka hada da ‘yan ta’adda da masu kai musu bayanai, kwanaki kadan da mummunar musayar wutar da aka yi tsakanin sojoji da ‘yan bindigar a wasu yankunan jihar Zamfara.
Jaridar PRNigeria ta rawaito, sojoji 10 na daga cikin wadanda suka mutu a lokacin da ‘yan bindigar suka fantsama garuruwan da ke kusa da yankin.
A ranar Litinin ma PRNigeria ta rawaito dakarun rundunar Operation Hadarin Daji, sun yi nasara kan ‘yan bindigar a kauyen Malele da ke karamar hukumar Dansadau a jihar Zamfara.
Sumame ta sama da sojojin sama suka kai a ranar Asabar ya yi nasarar hallaka gwamman ‘yan fashin dajin ciki har da wasu manya daga cikinsu.
An samu karuwar hare-haren ‘yan ta’adda a jihar Zamfara, sakamakon yadda sojojin suka fatattake su daga inda suke buya, sumamen da aka kai garuruwan Malele, Maigoge, Yan Sawayu, Ruwan Tofa, Mai Awaki, and Zama Lafiya, da ke karkashin gundumar Mutunji a karamar hukumar Dansadau sun kara kai mi.
‘Yan fashin daji da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da zama babbar barazana a jihar Zamfara, inda suke haddasa rasa rayuka da dukiya, ko da yake gwamnatin jihar da jami’an tsaro na cewa su na bakin kokarin magance matsalar.