fidelitybank

An gano gawarwaki 15 a ambaliyar Borno -NEMA

Date:

Muhammad Usman, Kodinetan Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) a shiyyar Arewa maso Gabas, ya ce, kimanin gawawwaki 15 ne aka gano a kogin Ngadabul da ya mamaye birnin Maiduguri na jihar Borno.

Ya bayyana cewa, ambaliyar ta shafi al’ummomi da dama da ke gabar kogin Maiduguri.

Da yake magana da manema labarai a Maiduguri a ranar Laraba, ya shawarci iyaye da masu kula da su da su gargadi ma’aikatansu da ‘ya’yansu game da yin iyo a cikin kogin don gudun kada a nutse.

Usman ya bayyana cewa NEMA a matsayinta na hukumar kula da bala’o’i ta kasance tana wayar da kan al’umma kan hadurran da ke tattare da ambaliya da matakan kariya.

Ya kara da cewa, “Mun yi ta ganawa da masu ruwa da tsaki daban-daban kan wayar da kan jama’a da kuma samar da kayayyakin agaji ga al’ummomin da abin ya shafa.”

Hakazalika, domin dakile al’amuran mutanen da aka nutse a ruwa, rundunar jami’an tsaron farin kaya ta Jihar Borno ta tura jami’anta a bakin kogin domin fatattakar yaran da ke zuwa rafi domin yin iyo.

spw

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp