Masu bincike, sun gano shaidar gashin tsuntsu a jirgin saman da ya yi hatsari a Koriya ta Kudu a watan Disambar 2024, inda mutane 179 suka mutu.
An gano gashin da kuma alamun jini a cikin injinan jirgin saman mallakin kamfanin Jeju. Gashin ya yi kama da wani tsuntsu mai yanayi da agwagwar ruwa kamar yadda masu binciken su ka bayyana da kuma aka wallafa rahoton a ranar Litinin.
Binciken da ake yi kan musabbabin hatsarin jirgin mafi muni da Koriya ta Kudu ta fuskanta a dan tsakanin nan, zai maida hankali kan rawar da tsuntsun ya taka ta hanyar shigewa cikin injin Jirgin a lokacin da ya fadi.
Za dai an cire injin jirgin samfurin Boeing 737-800, da kankaren da ke kan titin jirgin domin sake gano karin bayani kan hatsarin jirgin saman.