Tsohon Babban Bankin Najeriya, CBN, Gwamna Godwin Emefiele, ya yi amfani da biliyoyin Naira ba bisa ka’ida ba a cikin asusun banki kusan 593 a kasashen Amurka, Ingila da China.
Mai bincike na musamman na shugaban kasa Bola Tinubu, Jim Obaze, ya bayyana cewa Emefiele ya bude asusun ajiyar banki ba tare da amincewar kwamitin gudanarwa da saka hannun jari na CBN ba.
Obaze ya bayyana cewa Emefiele ya ajiye kudi 543, 482,213 a asusun ajiya a bankunan kasar Birtaniya kadai ba tare da izini ba.
Wannan yana kunshe ne a cikin rahoton karshe na Obaze mai lakabin, ‘Rahoton Bincike na Musamman akan CBN da Abubuwan da ke da alaƙa da aka mika wa Tinubu.
Rahoton ya kara da cewa: “Tsohon gwamnan CBN ya zuba kudin Najeriya ba tare da izini ba a wasu asusu 593 na kasashen waje a Amurka, China da Ingila a lokacin da yake rike da mukamin.
“Dukkan asusun da aka yi biliyoyin kudaden, duk mai binciken ne ya gano su, a kasar Burtaniya kadai, Emefiele ya ajiye kudi fam 543,482, 213 a cikin makudan kudade ba tare da izini daga hukumar CBN da kwamitin zuba jari na bankin ba.”
A halin yanzu dai tsohon gwamnan na CBN yana gidan yarin Kuje bayan da gwamnatin Najeriya ta gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zarginsa da almundahanar naira biliyan 1.2 na sayan sa.
Wata babbar kotun birnin tarayya Abuja ta bayar da belinsa a kan kudi N300m amma ya kasa kammala shi.


