Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan rasuwar Fatima, ‘yar shekara 13, daliba a ajin JSS II na makarantar Sheikh Bashir Isyaka Rabiu Girls Secondary School, Goron Dutse, Kano.
Mutuwar marigayiyar a unguwar Dandinshe Yamma, karamar hukumar Dala, ta girgiza al’umma tare da jefa su cikin tunanin tambayoyin tsaro da adalci.
A cewar iyalan ta, ranar Asabar ne suka shirya ziyarar gidauniyar wani aboki da ya mallaki sabon gida. A lokacin shirin tafiya, Fatima ta sanar da mahaifiyarta cewa za ta koma gida domin yin wanka kafin ta biyo su. Daga baya mazauna unguwa sun tabbatar da ganin ta tsaye a bakin ƙofa, wannan ne karon ƙarshe da aka gan ta da rai.
Da iyalin suka dawo daga tafiya, Rahila, babbar ‘yar gidan, ta fara ƙoƙarin shiga amma ƙofar ta kulle daga ciki. Mahaifiyarsu, Malama Madina Inuwa Makwalla, ta gwada buɗe ƙofar ba. Daga bisani mahaifinsu, Malam Sulaiman, ya dawo daga kasuwa, ya gwada shi ma bai samu ba, sai ya haura.
Abin da ya gani ya girgiza shi, ya tarar da ‘yarsa Fatima rataye a taga, wuyanta a karye. Kiran taimako ya sa mazauna unguwar suka taru, amma duk sun bayyana cewa abin ya ba su alamar akwai lauje cikin nadi.
‘Yan sanda sun isa wurin da gaggawa, suka dauki gawar zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad. Bayan bincike, likitoci sun tabbatar da cewa ba a yi wa marigayiyar fyade ba, amma an karya wuyanta kafin a rataye ta, abin da ya kara tabbatar da shakku cewa ba ta kashe kanta ba.
An mika gawarta ga iyali, inda aka yi mata jana’iza bisa tsarin musulunci.
A wata hira da Daily Trust, mahaifiyarta, Malama Madina, wacce ita ma malamar makaranta ce a Kano, ta bayyana Fatima a matsayin ‘ya mai biyayya, natsuwa da kauna. “Fatima ba wai ‘yata ce kawai ba, abokiya ce a wajena. Rashinta ciwo ne da ba zai taba warkewa ba,” in ji ta cikin hawaye.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa bincike na ci gaba. “Mun karɓi kiran gaggawa daga iyali, muka garzaya muka dauki matakan da suka dace. Bincike mai zurfi ya fara domin gano gaskiyar lamarin da kuma tabbatar da adalci,” in ji shi.
Lamarin ya girgiza mazauna Dandinshe Yamma, inda suka ce Fatima daliba ce mai ladabi da fara’a da kowa ke kauna. “Mutuwarta ta bamu ciwo sosai. Muna rokon hukumomi su tabbatar da an gano gaskiya,” in ji wani mazaunin unguwar, Aminu Garba.