Masu shirya kyautar Ballon d’Or, sun fitar da jerin sunayen ‘yan wasa da za su fafata a na lashe kyautar Kopa ta 2025.
Za a ba da kyautar ga mafi kyawu ‘yan kasa da shekaru 21.
Wasu fitattun sunayen da ke cikin jerin sun hada da Lamine Yamal (Barcelona), Desire Doue (Paris Saint-Germain) da Dean Huijsen (Real Madrid).
Sauran sun hada da mai tsaron baya na Arsenal, Myles Lewis-Skelly da Estevao Willian, wanda ya koma Chelsea kwanan nan daga Palmeiras.
Za a sanar da wanda ya yi nasara a wani taron a ranar 22 ga Satumba.
Sunayen ‘yan wasan
• Myles Lewis-Skelly
• Rodrigo Mora
• Joao Neves
• Lamine Yamal
• Kenan Yildiz
• Ayyoub Bouaddi
•Pau Cubarsi
• DĂ©sirĂ© DouĂ©
• Estevao
• Dean Huijsen