Al’ummar Iran sun fara taruwa a biranen kasar domin nuna girmamawa ga Shugaba Ebrahim Raisi, bayan da ya mutu tare da ministan harkokin wajen a hatsarin jirgin sama a wani yanki mai tsaunuka a arewa maso yammacin kasar ranar Lahadi.
A jiya Litinin ne babban jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei ya bayar da sanarwar kwanaki biyar ta zaman makoki. An kuma dakatar jarrabawar daliban makarantun kasar.
Ana kuma shirye-shiryen zaben sabon shugaban kasa da za a gudanar zuwa ranar 28 ga watan Yuni.
Da fatan za a kasance da mu yayin da muke kawo muku sabbin labarai daga kasar Iran.