Al’ummar Kenya sun fara fita rumfunan zaɓe, don zaɓar wanda zai maye gurbin Shugaba Uhuru Kenyatta, wanda ya shafe wa’adi biyu yana mulkin ƙasar.
Mr Kenyatta na goyon bayan tsohon abokin hamayyarsa ne Raila Odinga, a maimakon mataimakinsa William Ruto.
Matsalar durƙushewar tattalin arziƙi da dimbin bashin da ake bin Kenya, na daga cikin abubuwan da duk wanda ya lashe zaɓen zai ji da su.
Masu sharhi na ganin kawancen Kenyatta da Odinga zai haɗa kan ƙasar, la’akari da cewa sun fito ne daga ƙabilu daban-daban.
Bayan zaɓen Shugaban kasa, masu jefa kuri’ar kazalika za su zaɓi gwamnoni da ƴan majalisa. A cewar BBC.