Hukumar jin daɗin alhazai ta birnin Tarayyar Abuja ta ce, za ta fara gudanar da bincike lafiya ga maniyyatan bana daga 5 ga watan Mayu zuwa 7 ga watan.
Daraktan hukumar Malam Abubakar Evuti ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar Malam Muhammad Aliyu ya fitar a ranar Talata.
Evuti ya ce za a fara yi wa maniyyata aikin hajjin bana allurar riga-kafi daga 15 ga watan na Mayu zuwa 17 ga watan, saboda a samu kammala shirye-shiryen maniyyatan da wuri.
Ya kuma shawarci maniyyatan da su tabbatar sun yi duka abubuwan da hukumar ta shirya yi domin ba su damar gudanar da aikin hajjin yadda ya kamata.
Ya kuma ja kunnen waɗanda har yanzu ba su mayar da fom dinsu ba da su hanzarta yin hakan ta hanyar kai fasfo ɗinsu.