Daya daga cikin jami’an kasar Ukraine da ke tattaunawa da takwarorinsu na Rasha, wanda kawo yanzu ake zagaye na hudu, ya shaida cewa an fara tattaunawa tsakanin juna ta hanyar alon kallo maimakon kai tsaye.
Jami’in mai suna Mykhailo Podolyak ya ce, bangarorin biyu sun bayyana wa juna matsayarsu kan yakin da ake gwabzawa.
Tun da farko ya ce, tattaunawar za ta fi mayar da hankali kan tsagaita wuta da kuma janyewar dakarun Rasha, baya ga tabbatar wa Ukraine cewa, ba za a sake daukan matakan yaki irin na yanzu a kanta ba.