fidelitybank

An fara tattara sakamakon zabe a Adamawa

Date:

Wasu malaman zaɓe sun koma babban ofishin hukumar zaɓe na INEC da ke Yola bayan shafe yinin ranar Asabar a bakin aiki a sassa daban-daban na jihar Adamawa.

Ma’aikata da kuma jami’an tsaro sun yi cirko-cirko a ofishin na INEC inda suke jiran a fara amsar takardun kaɗa kuri’a da kuma sauran kayayyakin zaɓe da suka dawo da su.

Ya zuwa safiyar Lahadi, babban ɗakin da hukumar zabe a Adamawa ta tanadar domin karɓar sakamakon zaɓen daga kananan hukumomi ya kasance fayau domin kuwa babu kowa cikinsa sai masu gadi.

Duk da yake a shelkwatar ta INEC ta jiha, ba’a fara bayyana alƙaluman zaben ba, to amma an shafe tsawon dare ana tattara shi a ofisoshin hukumar zaɓe na wasu daga cikin ƙananan hukumomi 21 da ke jihar ta Adamawa.

Rahotanni dai sun nuna cewa zaɓen ya kammala a ko’ina a Adamawa ba tare da wata hatsaniya ba.

daily post nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp