Hotunan tallata gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed a matsayin shugaban kasa a 2027 sun bayyana a kan titunan Bauchi, dauke da taken “Kaura ga shugaban kasa 2027.”
An ga fastocin a wurare masu mahimmanci da suka hada da zagayawa, sandunan lantarki, da allunan da ke kan manyan tituna kamar titin Railway, Sabon Titin Karofi, da Titin Kofar Dumi.
Daya daga cikin matasan da suka yi aikin lika fastocin, Aminu Auwal, ya ce wasu ‘yan siyasa biyu ne suka dauke su aiki.
“An umurce mu da mu sanya allunan gwamnan a kan manyan titunan jihar Bauchi, mun fara aikin ne da misalin karfe 1 na safiyar yau kuma muna fatan kammala shi a yau,” inji Auwal ya shaida wa daily trust.
Mutanen da aka ruwaito sun kaddamar da aikin an bayyana sunayensu da Ya’u Ortega da Talolo, sai dai kokarin jin ta bakinsu ya ci tura domin lambobin wayarsu ba ta hade ba.