Hukumar Alhazan Najeriya ta fara shirhin aikin hajjin 2026 mai zuwa, jin kaɗan bayan kammala aikin hajjin bana.
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Pakistan ne ya bayyana haka lokacin ganawa da manema labarai ranar Alhamis a Kano.
“Mun samu umarni daga hukumomin Saudiyya cewa kowace ƙasa ta hanzarta tsara shirin aikin Hajji mai zuwa domin kuwa ba za su lamunci jinkiri ba;” in ji shi.
Shugaban hukumar ya ce yanzu abin da suke jira shi ne amincewar hukumomi kan kuɗin kujerar aikin hajjin 2026, domin sanar wa maniyyata.
A shekarar da ta gabata dai alhazan Najeriya sun biya naira miliyan takwas da ɗoriya.
Farfesa Pakistan ya yi kira ga maniyyan ƙasar su hanzarta biyan kuɗin da zarar hukumar ta bayyana kuɗin kujera.