Gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa ‘yan kasar cewa, an fara sayar da shinafa mai nauyin kilo 50 a kan kudi Naira 40,000 a sassan kasar nan.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris ne ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida yayin ganawa da manema labarai ranar Laraba a Abuja.
Ministan ya bayyana cewa an raba shinkafa a wuraren da aka kebe har zuwa lokacin da za a fara siyar da ‘yan Najeriya.
A cewarsa, gwamnati na ci gaba da bayyana hanyoyin da za a bi domin ganin cewa ba za a yi awon gaba da sayar da shinkafar da wasu mutane ba.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati za ta bai wa ‘yan Najeriya cikakkun bayanai kan cibiyoyi a fadin kasar inda za su iya samun kayayyakin a kan wannan farashi.
“Zan iya tabbatar muku da cewa ana samun shinkafar kan Naira 40,000 kan kowace buhu mai nauyin kilo 50. Za a sayar da shi a cibiyoyi daban-daban a fadin kasar.
“Za mu ba ‘yan Najeriya cikakkun bayanai kan wuraren da aka siyar da su da zarar an fara siyar da su.
“Ana yin taka-tsan-tsan don kada wadanda ke da kudin saye da yawa su yi awon gaba da shi tare da yin amfani da wadanda ake so su samu,” in ji shi.
Bayanin na Ministan ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan cewa har yanzu ba a samar da kayan a kasuwannin Najeriya kan Naira 40,000 kan kowacce buhu ba.
Idan za a tuna a ranar Litinin ne gwamnati ta sanar da rage farashin buhun shinkafa da kashi 50 zuwa N40,000 kan kowace buhu 50, yayin da ta yi kira ga ‘yan kasar da su guji zanga-zangar ranar 1 ga Agusta, 2024.


