Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta tabbatar da cewa an fara aikin “sada mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma wadanda Isra’ila ke tsare da su da danginsu”.
Kungiyar dai zuwa yanzu ba ta tabbatar da ko mutum nawa ne jami’anta suka karba ba, sai dai ta bayyana aikin a matsayin wani al’amari mai “gabobi da yawa a rana guda” wanda zai kunshi tabbatar da kai kayan agaji zuwa Gaza.
Muna sa ran samun karin bayani daga Red Cross, da cikakken bayani a kan adadin mutanen da aka sako, nan gaba a yau.