Jihar Jigawa ta samu ruwan sama na farko a daminar shekarar 2023, inda aka samu saukin yanayin zafi.
Hakan ya ba mazauna yankin dadi sosai, bayan sun sha fama da zafi na tsawon wata daya da cizon sauro.
DAILY POST ta lura cewa mazauna yankin sun yi marhabin da ruwan sama cikin murna da annashuwa a kusan dukkan sassan jihar tare da fatan damina ta rage musu radadi.
Sai dai ruwan sama ya sha banban a wasu sassan jihar a yammacin Lahadi da dare wanda ya dauki tsawon mintuna 15 zuwa 30.
Malama Aisha, wata matar aure a garin Ringim ta ce ruwan sama ya sanyaya zafin da ake gani a yankin na tsawon lokaci.
“Tare da wannan ci gaban, yanzu muna kwana a gida cikin kwanciyar hankali ba tare da damu da yanayin zafi ba,” in ji ta.
Haka kuma, wasu daga cikin manoman da suka zanta da DAILY POST, sun bayyana jin dadinsu da wannan ci gaban.
Malam Abdullahi, wani karamin manomi a Dutse, ya ce duk da ruwan sama ya dan makara idan aka kwatanta da daminar bara, ya riga ya kwashe gonarsa yana jiran damina.
“Idan damina ta ci gaba a haka na tabbata nan da wasu kwanaki za mu fara dasa shuki cikin lokaci,” in ji shi.
Sai dai ya bukaci gwamnatoci da su shirya tunkarar damina tare da tallafa wa manoma tare da daukar matakan da suka dace domin kaucewa ambaliyar ruwa.