Sakamakon fara zaɓe a kan lokaci da kuma fitowar masu zaɓen da wuri, yasa an fara gudanar da zaɓukan da aka tsara gudanarwa a yau Asabar a wasu kananan hukumomi a kan lokaci a Kano.
Wakilin BBC ya tabbatar da cewa a mafi yawan wurare an fara zaɓen kamar yadda aka tsare a wasu wuraren kuma an samu jinkiri.
Daya daga cikin wuraren da aka fara zaɓen a kan lokaci shi ne ƙauyen Tukwui a karamar hukumar Makoɗa.
Karanta Wannan: A na gudanar da zaɓen da bai kammala na a Adamawa
A wata mazaɓa a ƙauyen tuni aka kammala ƙada ƙuri’a a wata a kwatu mai mutum 60.
A ƙaramar hukumar Makoɗan an samu hargitsi a wasu wuraren kan amincewa da inda za a ajiye akwatin zaɓen da za a kaɗa ƙuri’ar cikinta


